Odinga: Babu raba madafun iko a Kenya
September 3, 2017Talla
Jagoran adawa a kasar KenyaRaila Odinga ya bayyana cewa ba zai shiga shirin raba madafun iko ba da gwamnatin da ke mulki a kasar yanzu. Odinga ya bayyana haka ne a wannan rana ta Lahadi kwanaki biyu bayan da kotun koli ta soke nasarar da Shugaba Uhuru Kenyatta ya yi a zaben watan Agusta ta kuma bada umarni na a sake zabe cikin kwanaki 60.
Dukkanin bangarorin biyu dai sun ja daga a shirin fita sake fafatawa a zabe inda za a sake gwarawa tsakanin Uhuru Kenyatta dan shekaru 55 da jagoran adawa Odinga dan shekaru 72, dukkanin bangarori biyun dai sun shiga yanayi na ci gaba da karta kasa.