1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wajibi ne a gyara dokar zabe

Zainab Mohammed Abubakar
October 14, 2017

Mutane biyu ne suka rasa rayukansu ka na wasu suka ji raunuka, biyo bayan arangama tsakanin jami'an 'yan sandan Kenya da masu zanga-zangar nuna goyon baya ga madugun adawa Raila Odinga.

https://p.dw.com/p/2lpyf
Kenia Raila Odinga, Oppositionsführer | Interview in London, Großbritannien
Hoto: Reuters/P. Nicholls

A hirar da radiyon DW ta yi dashi Raila Odinga ya ce, ya janye daga takararce saboda bashi da wani zabi, kasancewar hukumar zabe da ma gwamnati sun kudiri aniyar kin bin umurnin kotun kolin kasar.

Rikici ya barke tsakanin masu gangamin adawa da jami'an tsaaro a sassa daban daban na Kenyan, musamman yankin yammacin kasar da ya ke da dumbin magoya baya. Sai dai acewarsa wannan tashin hankali bashi da alaka da janye takararsa..

" Ko kadan janyewa daga takara da na yi bashi da nasaba da rudanin da kasar ke ciki. Dokar a bayye ta ke, bisa ga zartarwar kotun koli a shekara ta 2013 wanda ke nunar da cewar, idan daya daga cikin 'yan tajkarar, walau zababben shugaban ko kuma mai kalubalantarsa, wanda shi ne ya shigar da kara, ya kauracewa zaben, to babu wani zabe da za'a gudanar. Dole ne hukumar zabe ta kasa ta fara sabon shirye shiryen zaben 'yan takara domin gudanar da sabon zabe".

Kenia Nairobi Demonstration Odinga Anhänger
Gangamin magoya bayan Odinga Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Hakan na nufin babu wani zabe da za'a gudanar a kasar ta Kenya kamar yadda aka tsara a ranar 26 ga wannan wata na Oktoba. Raila Odinga ya musanta zargin da ake masa  na rashin gabatar da takardar janyewarsa daga zaben a hukumance.

"Ban san me suke nufi da janyewa a hukumance ba, domin na gabatar da wasikar da ke nuna janyewata, kuma sun tabbatar da samun wasikar. Ban san me suke son nunawa ba, su ne sane da cewar na janye domin na gabatar da wasika, kuma sun samu".

Dangane da ko ya damu da hali na tashin hankali da kasar Kenya za ta iya fadawa ciki ganin cewar 'yan adawa na cigaba da yin bore musamman a manyan biranen Kenya, madugun adawar Odinga ya kada baki da cewar.

Kenia Nairobi Demonstration Odinga Anhänger
Zanga-zangar 'yan adawa a NairobiHoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

"Ko shakka babu zai zama abun takaici idan an samu barkewar rikici a kasar. Al'umar Kenya mutane ne da ke son zaman lafiya. Basa son tashin hankali. Barkewar rikici na nufin samun damar gwamnati na amfani da bindiga ko barkonon tsohuwa akan mutanen da basu ji ba basu gani ba da ke bayyana korafinsu. Kundin tsarin mulkin kasa ya bawa jama'a 'yancin yin gangami, ba wai alfarma ce daga gwamnati ba".

Zanga zangar da 'yan adawn ke gudanarwa dai ya sabawa sabon umurnin gwamnatin Kenyan na haramta ta a manyan cibiyoyin kasuwancin kasar guda uku..))