Odinga ya kira zanga-zanga a ranar zabe
October 18, 2017Raila Odinga a yayin jawabinsa ya ce gangamin na ranar 26 ga wannan watan na Oktoba zai kasance wanda ba a taba gani ba a kasar, a makon da ya gabata dan takarar kujerar shugaban kasar ya sanar da janye takararsa a zaben da aka bukaci maimaitawa bisa wasu manyan kura-kurai, sakamakon zaben na farko ya bai wa shugaba mai ci Uhuru Kenyatta nasara.
A daya bangaren kuwa, hukumar zabe a wannan Laraba ta gargadi 'yan takara da ma sauran shugabani na jam'iyyun siyasa da su guji tsoma baki cikin lamurran hukumar a yayin da ta ke kokarin ganin ta gudanar da sahihiyar zabe, shugaban hukumar Wafula Chebukati ya yi gargadin ne a yayin ganawa da manema labarai gabanin zaben na mako mai zuwa inda ya nuna yatsa ga jagororin jam'iyyun siyasa a kenya da ya ce sun kasance babban barazana ga demokradiyar kasar.