1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Odinga ya yi kiran kauracewa zaben Kenya

Ramatu Garba Baba
October 25, 2017

Jagoran jam'iyyar adawa a Kenya Raila Odinga ya yi kira ga magoya baya da su kauracewa zaben shugaban kasar da zai gudana a gobe Alhamis, acewar sa babu abinda ya sauya a tsarin hukumar kan gudanar da sahihiyar zabe.

https://p.dw.com/p/2mV4W
Kenia Wahl Politiker Raila Odinga vor Anhängern
Hoto: Reuters/B. Inganga

Dubban magoya bayan Raila Odinga daga lungu da sakon kasar sun amsa kiran gwanin nasu da ya janye daga takarar shugabancin kasar bayan fitar da sanarwar sake zaben da aka soke bisa zargin cewa an tafka kura-kurai da suka sabawa doka.

Mahunkunta kasar sun ce zaben shugaban kasar zai gudana kamar yadda aka tsara duk kuwa da takaddamar da ke tattare da zaben da a sakamakon farko ya bai wa shugaba mai ci Uhurru Kenyatta nasara. Babban kotun kolin kasar ya sanar cewa an gagara saurarar kara da aka shigar a gaban kotun na neman dage zaben, alkalin kotun David Maraga ya ce su biyu kacal suka halaci zaman ba tare da ya yi karin bayani kan dalilan da suka hana sauran halarta zaman ba.

A wannan Laraba daruruwan mutane wadanda akasarinsu mata ne sun gudanar da gangami don yin kira ga sauran al'ummar kasar  da su rungumi zaman lafiya su kuma guji duk wani abu da zai haifar da rikici a wannan yanayi da kasar ta samun kanta ciki. A baya kotun koli ta yanke hukuncin soke zaben shugaban kasar na farko da ya gudana a watan August da ya gabata bayan wasu kura kurai da aka samu da aka ce sun sabawa doka, rahotannin daga kasar na cewa al'umma na zaman dar-dar a kasar da tayi kaurin suna wajen rikice rikice a yayin zabe ko bayan fidda sakamako..