Afirka za ta karbi bakuncin Scholz
April 28, 2023Talla
Kakakin fadar gwamnati Christiane Hoffmann ce ta bayyana hakan, inda ta ce shugaban gwamnatin Jamus din Olaf Scholz zai kasance a Afirka daga ranar hudu zuwa shida ga watan Mayu mai zuwa. Ziyarar ta Scholz dai, za ta mayar da hankali ne a kan yaki da yunwa da sauyin yanayi da hadin kan tattalin arziki da wanzar da zaman lafiya da sasanta rikici kamar wanda a yanzu haka ake fama da shi a Sudan. Yakin basasar da aka kwashe tsawon shekaru biyu ana gwabzawa a yankin Tigray na Habasha dai, ya yi sanadiyya mutuwar daruruwan mutane kafin a kai ga kawo karshensa bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Nuwambar bara.