OPEC: Babu kari kan abin da muke fitarwa
May 25, 2017Talla
Ministocin da ke wannan kungiya suka bayyana haka bayan zaman da suka yi a birnin Vienna a wannan rana ta Alhamis inda suka ce za su zauna kan adadi da suke..
Kasashe mambobin wannan kungiya da wasu kasashe 11 da ke fitar da man na fetir karkashin jagorancin Rasha na fitar da man fetir da rage ganga miliyan daya da dubu 800 a kowace rana tun daga watan Janairu a kokari na samar da yanayi da farashin na mai zai inganta.
A cewar ministan mai na Iraki Jabbar Ali Hussein al-Luiebi, wannan mataki na sake daukar watanni tara a kan abin da suke fitarwa na gangar mai a kowace rana zai taimaka masu wajen samun daidaito a kasuwa.