OPEC zata rage yawan mai da ta ke haka da garwa dubu 500 a rana
December 14, 2006Talla
Daga watan janeru mai zuwa kasar Angola zata zama memba ta 12 a cikin kungiyar kasashe masu arzikin man fetir a duniya wato OPEC. An bayyana haka ne a sanarwar bayan taro da ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar suka yi yau a birnin Abujan Nijeriyya. Da farko an so daukar Angola cikin kungiyar ne a cikin watan maris. Bugu da kari taron ya kuma amince da rage yawan man da kungiyar ta OPEC ke hakowa da ganga dubu 500 a ko wace rana daga watan fabrairu. Jim kadan bayan ba da wannan sanarwa farashin danyan mai ya tashi a kasuwannin mai na duniya.