1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

P/M Isra'ila na kwance rai hannun Allah

January 5, 2006

An sake kwantar da Ariel Sharon a asibiti sakamakon ciwon bugun zuciya

https://p.dw.com/p/Bu2h
Ariel Sharon
Ariel SharonHoto: AP

A lokacin da cutar bugun zuciyar ta rutsa da P/M Isra’ila Ariel Sharon a karo na farko, mukarrabansa sun ba wa likitoci shawara a game da bayyana wa jama’a bayani dalla-dalla a game da ciwon da yake fama da shi tare da ikirarin cewar babu wani abin damuwa game da makomar lafiyarsa. An yi hakan ne domin kwantarwa da jama’a hankalinsu ta la’akari da yakin neman zaben da tuni aka gabatar a kasar Isra’ilar. Amma fa sake bugawar zuciyar tasa karo na biyu a yammacin jiya laraba, a yanzun likitocin ba su da ikon ikirarin cewar babu wani abin damuwa a game da makomar lafiyar P/Mn mai shekaru 78 da haifuwa. Ko meine ne dai ake ciki, bisa ga dukkan alamu Schron ba zai sake komawa gadan-gadan domin a rika damawa da shi a harkokin siyasa ba, lamarin da ba shakka zai yi tasiri akan zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 28 ga watan maris mai zuwa da kuma makomar shawarwarin sasanta rikicin yankin gabas ta tsakiya. A dai cikin shekaru biyar da suka wuce P/Mn na Isra’ila ya taka muhimmiyar rawa mai tasirin gaske a al’amuran yankin gabas ta tsakiya. Ya dauki matakai iri daban-daban masu tsananin gaske akan Palasdinawa da wulakanta abokin gabarsa marigayi Yasser Arafat yana mai kusantar da kansa ga shugaba George W.Bush tare da nuna taurin kai da watsi da kudurori na kasa da kasa da yin ko oho da kiraye-kiraye daga Amurka domin nuna halin sanin ya kamata bisa manufa.

Wannan maganar ta shafi gaban kansa da Sharon yayi game da janyewa daga zirin Gaza. A wannan bangaren P/Mn sai da ya shiga takun-saka da wakilan jam’iyyarsa ta Likud. Bayan da ya gaji da wannan sabani, Sharon ya bijire wa jam’iyyar ta Likud ya kafa tasa jam’iyyar mai suna Kadima, dake ma’anar gaba dai gaba, wadda aka yi hasashen cewar tana da kyakkyawar dama ta lashe zaben na watan maris mai zuwa. Amma tilas ne a saka ayar tambaya a game da makomar jam’iyyar ta Kadima, saboda Sharon shi ne wuka da nama, kuma mukarrabansa dake ba shi goyan baya da wuya su iya samar da wani ci gaba na a zo a gani ga wannan jam’iyyar in har an rasa Sharon. Ita kuwa jam’iyyar Likud, tsofon P/M Natanyahu ne ke mata jagora, mutumin da bayyana adawar janyewar Isra’ila daga Gaza ya kuma sa kafa yayi fatali da yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo. Ita kuma jam’iyyar adawa ta Labour babu wata muhimmiyar rawar da zata iya takawa a yanzun saboda sabon shugabanta Amir Peretz baya da fice a harkar siyasa. A lokaci guda kuma a daya hannun ana ci gaba da fama da yamutsin siyasa tsakanin Palasdinawa, inda suke shawarar dage zaben da aka shirya a karshen wata. Watakila mafi alheri shi ne dukkan Isra’ilawan da Palasdinawa su dage zaben nasu ta yadda zasu samu ikon shawo kann matsalolinsu na cikin gida.