Palasdinu: Kungiyar PLO ta yi watsi da Isra'ila
January 16, 2018Talla
A kasar Palasdinu kwamitin gudanarwa na kungiyar kwatar 'yancin lasar Palasdinu wato PLO ya dauki mataki dakatar da amincewa da kasantuwar kasar Isra'ila a matsayin kasa, matakin ke a matsayin babban tuballin da aka kafa shirin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palasdinawan.
Kwamitin gudanarwa na Kungiyar ta PLO ya kada kuri'ar dawowa daga matakin amincewa da Isra'ila a matsayin kasa bayan wani taron kwanamki biyu da ya gudanar a birnin Ramalla na yammacin kogin Jodan a karkashin jagorancin shugaban Palasdinawan Mahmud Abbas. Wannan mataki na kungiyar PLO na a matsayin martani ga matakin da shugaba Trump na Amirka ya dauka a ranar shida ga watan Disambar da ya gabata na bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.