Paparoma: A dauki mataki kan sauyin yanayi
October 4, 2023Talla
Shugaban na Katolika na duniya ya yi gargadin cewa dumamar duniya na neman kaiwa matakin da ba za a iya sauya shi ba.
Paparoma Francis ya kara ankarar da al'umma a game da hadarin sauyin yanayin ga bil Adama da kuma ita kanta duniyar inda ya ce masu rauni a duniya su ne suka fi shan radadin dumamar yanayi.
Ya kuma tabo Amurka wadda ya ce yawan hayakin da ta ke fitarwa a shekara ya ninka abin da China ke fitarwa har sau biyu sannan ya rubanya har sau bakwai abin da kasashe masu tasowa suke fitarwa.
Jawabin na Paparoma na zuwa ne gabanin taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya COP 28 da za a yi nan gaba a Dubai