Paparoma Francis na shirin Kai ziyarar farko a Afrika.
November 24, 2015Talla
Jami'an tsaron kasar Kenya dai na shirin samar da dakarun tsaro har dubu goma a biranen Kasashen Kenya da Yuganda a yayin ziyarar Paparoma Francis wacce ta kunshi ganawa da talakawa.
Biranen Nairobi da Kampala dai na fuskantar hare-haren 'yan kungiyar Al-Qaeda dake a gabashin Afrika gami da kungiyar Al-shabbab bisa martani kan shiga yakin Somaliya da kasashen suka yi.
Babban jami'in 'yan sandan Kenyan dai ya tabbatar da cewar sun kammala dukkan wasu shirye-shiryen karbar bakuncin Paparoman da zai fara a ranar Larabar nan.