Paparoma Francis zai sha rantsuwar kama aiki.
March 19, 2013Yau aka shirya za a ƙaddamar da bikin rantsar da Paparoma Francis, sabon jagoran yan ɗarikar Roman Katolika, kwanaki shidda bayan zaɓen sa akan matsayin. Ana tsammanin dubun dubatan jama'a za su yi dafifi a dandalin Sainte Peter da ke a birnin Rome, domin hallarta adu'o'in da bikin rantsar da sabon Paparoma.
A cikin waɗanda aka shirya za su hallara sun haɗa da mataimakin shugaban ƙasar Amirka Joe Biden da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da na Faransa da Spain da kuma shugaba Robert Mugabe na Zimbabuwe. Duk kuwa da cewar ya na a ƙarkashin wani takunkumi na haramta yin zirga-zirga zuwa nahiyar Turai tun a shekarun 2002. An baza 'yan sanda da sojoji har kusan dubu uku a dandalin na Saint Peter domin kula da tsaro.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman