Paparoma ya yi kiran zaman lafiya da taimakon jinkai
December 25, 2024Masu aiko da rahotanni sun ce tun a ranar Talata mabiya addinin na masihiya suka fara haduwa a majami'ar Nativity, sai dai ba a ga irin adon da aka saba yi ba kuma wannan shi ne karo na biyu a jere ana yin bikin Kirsimeti a yanayi irin wannan.
Mazauna yankin sun ce mutanen da suka saba zuwa wajen bikin Kirsimeti daga sassan duniya daban-daban sun kaurace wa bikin saboda yanayin da ake ciki kamar yadda magajin garin Bethlehem Anton Salman ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya bukaci da a samar da wata dama da za ta taimaka wajen shigar da kayan agaji ga wadanda yaki ya daidaita a kasar Sudan.
A jawabinsa da ya saba yi a duka ranar Kirsimeti, Paparoman ya bukaci da a yi duk mai yiwuwa wajen ganin an shigar da kayan agaji Sudan din wadda ta shafe watanni kimanin ashirin tana fama da yakin basasa.
A hannu guda ya kuma bukaci a fara sabon zama da nufin ganin an cimma yarjejeniyar zaman lafiya a kasar wadda ake ci gaba da kai ruwa rana tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye.