Rasha ta ja kunnen Ukraine kan kai hari
June 7, 2018Talla
Duk da alwashin da ya sha na maida martani, shugaban na Rasha ya ce ya na fatan ba za a kai ga yin hakan ba amma kuma idan Ukraine ta kuskura ta kai hari a gabashin Rasha din to fa za ta dandana kudarta. Putin din na wadannan kalaman ne lokacin da ya ke amsa tambayoyin 'yan kasar a wani shiri na wayar tarho da aka haska a gidajen talabijin din kasar inda mai tambayar wanda dan aware ne daga yankin Donetsk ya bukaci sanin matakin da zai dauka in har aka kai hari a lokacin wasannin na kwallon kafa na duniya wanda za a fara a kasar a makon gobe.