Rasha ta yi barazanar tsinke iskan gas ga Turai
March 31, 2022Talla
Dokar ta tanadi cewar kasashen da ba su dasawa da Rasha da ke sayen makamashin iskan gas daga Rasha ya kamata su bude asusu a cikin bankunan Rasha don biyan kudin makamanshin da Rasha ke sayer musu da kudin Ruble daga wannan asusu wanda ya ce za a fara yin aiki da dokar ranar Juma'a. Putin ya ce idan wadannan kudaden ba a zuba su a cikin bankuna,ba za mu lura cewar abokanan cinikayarmu sun sabama alkawarinsu na cinikaya babu wanda ke sayar mana da wani abu kyauta. Haka nan ba za mu yi aikin agaji ba. Wannan yana nufin kwangilar da ake yi a halin yanzu zai kasance an dakatar da ita.