Putin ya yi tayin huldar mutunci da gaskiya da Amirka
December 30, 2017Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi wa takwaransa na Amirka Donald Trump tayin yin huldar mutunci da gaskiya tsakanin kasashen nasu biyu. Ya bayyana wannan bukatarsa ce a sakon barka da sabuwar shekara da ya aika wa Shugaba Trump din da ma sauran shugabannin duniya.
A sakon nasa zuwa ga Shugaba Trump, Shugaba Putin ya bayyana cewa kyakkyawar hulda tsakanin Rasha da Amirka a kuma cikin mutunci, abu ne da ke da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya baki daya.
Kazalika shugaba Putin ya aika sakon barka da shiga sabuwar shekarar ga wasu shugabannin kasashen duniya da suka hada da na tsaffin kasashen tsohuwar daular Soviet da Emmanuel Macron na Faransa, da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, da kuma musamman ga Shugaba Bashar al-Assad na Siriya wanda ya tabbatar wa da cewa Rasha za ta ci gaba da ba shi duk taimakon da kasarsa take bukata domin kare 'yancinta da kuma hadin kanta.