Rasha za ta kyautar hatsi ga Afirka
July 27, 2023Talla
Putin ya bayyana haka ne a jawabin bude taron da aka soma na kasashen Afirka da Rasha a Saint Petersburg da ke a arewa maso yammacin Rasha. ''A cikin watanni masu zuwa, za mu iya tabbatar da isar da hatsi tan dubu 25 zuwa dubu 50, kyauta zuwa kasashen Burkina Faso, da Zimbabwe, da Mali, da Somaliya, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Eritrea. Taron wanda za a kammala a gobe jumaa zai kuma tattauna batun tsaro da hulda tsakanin rasha da kasashen na Afirka.