Yunkurin rage karfin Amirka a tsaron Turai
November 10, 2018Talla
Shehuba Marcon wanda ke karban bakoncin shugabannin kasashen wadanda ke hallartan bikin zaman lafiya wanda ke gudanan a wani bangaren bikin cikar shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na daya, ya nuna cewa dogaro da Amirka ba mafita ba ce. Tun a jajiberin ganawarsu da Donald Trump ne dai, Emanuel Macron ya fada wa wata kafar yada labarai cewa, akwai bukatar kasashen Turai su kafa rundunar sojansu ta daban wanda babu hannun Amirka a ciki. Shi kuwa a nasa martanin Trump yace fadin hakan tamkar izgilanci ne ga Amirka. Shugabannin kasashen duniya da yawa ne ke hallalatar bikin wanda ke gudanan a birnin Paris.