Raguwar matsayin mutuwar yara
September 13, 2012Hukumar ta ce a cikin shekaru 20 da suka gabata an samu raguwar masayin mace-macen kananan yara da kashi 50 daga cikin dari. A cikin rahoton da ta gabatar a birnin New York hukumar ta ce a shekarar da ta gabata kananan yara miliyan shida da dubu 9o0 suka mutu kafin su isa shekaru biyar. A shekarar 1990 wato shekaru 22 da suka shude kuwa adadin yaran da suka mutu ya yi miliyan 12. To amma duk da haka kusan kananan yara maza da mata dubu19 ne ke mutuwa a kowace rana daga cututtukan da za a iya magance su. Babban darekton UNICEF, Anthony Lake ya ce za a iya ceton yara da dama ta yi musu riga kafin cututtuka da sama musu abinci mai kyau da kuma magunguna. Ya ce duniya tana da fasaha da ilimi za su iya samar da wadannan abubuwa.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mouhamadou Awal Bakarabe