1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rahotan UNICEF adangane da rayuwar kananan yara a turai

February 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuRj

Wani rahotan Asusun kula da ilimin yara kanana ta mdd na nuni dacewa yaran da suke kasashen Amurka da Britania sune a baya dangane da cigaban masanaantu.A wani rahotan data fitar wanda ya jera kasashen turai guda 21,adangane da halin da yara suke ciki bisa ga tsarin rayuwa,kasar Britania tazo ta karshe,inda Amurka ta dan dara ta kalilan.An dai yi laakari da halinda yaran ke ciki ne bisa,albsarkatu da suka mallaka da lafiyarsu da tsaro ,da harkokin ilimi ,da dangantakarsu ta iyalansu ,da kuma yanayin rayuwarsu da ababan dake musu barazana .

Kasar Holand ce dai take gaba dangane da kyautata rayuwar yara kanana,Bisa ga kiyasin wannan rahoto na mdd dai kasashen dake tsakiyar turai ne suka samu matsayi na shidan farko,kasar Spain tazo ta biyar ayayinda jamus tazo ta 11 kana Faransa ta samu matsayi na 16.