Rahoton shekara na hukumar Unicef
December 14, 2005Rahoton na asusun tallafawa kana nan yaran na Mdd,wanda keda taken wariya da wanda ba a iya gani, yayi kakkausar suka ga wasu gwamnatoci dake sakaci wajen inganta rayuwar kana nan yaran, wala Allah da gangan ko kuma ana sani, wanda hakan a cewar rahoton yana taimakawa wajen kara jefa kana nan yaran cikin mawuyacin hali na rayuwa.
Rahoton wanda bisa al´ada ke fita shekara shekara, yaci gaba da cewa daga cikin hasashen da akayi na cewa ana haifar yara miliyan 150 a kowace shekara a fadin duniya baki daya,kusan kashi daya bisa uku na wannan hasashen ba a yi musu rijistar haihuwa,kuma sannan yawan su na kara karuwa.
Yiwa yara rijista idan an haifesu a cewar rahoton shine zai dasa danba na sanin yawan yaran dake kasa da kuma matsalolin dake addabar su, wanda hakan ka iya bada kafar daukar matakin shawo kann abun ba tare da wani bata lokaci.
Rashin yiwa yaran da aka haifa rijista kuwa a cewar rahoton ,shine yake tabbatar da cewa ba a san da yaran ba a hukumance, ballantana kuma a dauki wani mataki na inganta rayuwar tasu.
Bisa ire iren wadannan matsaloli kuwa rahoton ya shaidar da cewa yara kusan miliyan daya da digo 2 ne ake safarar su kamar hajja, wasu kuma miliyan miliyan biyar da digo 7 ke tsintar kansu a hali na bauta, kana wasu miliyan daya da digo takwas ke samun kansu a sana´oi dake da nasaba da yan yawon dandi, kana a karshe wasu yaran masu yawan gaske ke tsintar kansu a mawuyacin hali na rayuwa.
Ba a da bayan haka, rahoton ya kuma yi tsokavi game da irin yawaitar yaran da ake samu ba iyaye, a sakamakon rasuwar iyayen ta hanyar cutar Kanjamau a hannu daya kuma da yadda ake tursasawa wasu yaran da dama yin Auren dole a wasu kasashe maso tasowa.
A cewar daya daga cikin jami´ai na hukumar dake bawa yara kariya, wato Karin Landgren,wannan kididdiga ta sama nada yawan gaske, amma abin yi shine a fito fili a bayyanawa duniya irin halin da wadan nan yara ke ciki tare da janyo hankalin gwamnatocin da abin ya shafa wajen daukar matakan da suka dace don inganta rayuwar manyan goben.
Shi kuwa Mr Anthony, daga daga cikin jami´an wannan hukuma ta Unicef , cewa yayi ba wai kawai gwamnatoci ne keda alhalin hakan ba harma da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma masu fada a cikin alumma,wanda dukkannin su nada muhimmiyar rawar da zasu taka wajen cimma wannan buri da aka sa a gaba.
Bugu da kari rahoton na wannan shekara ya kuma bukaci gwamnatoci dasu kara azama wajen daukar matakan da suka dace don hana ci gaba da yawaitar mutuwar yara dake kasa da shekara biyar a sakamakon matsaloli da za a iya yin maganin su. San nan a daya hannun rahoton ya bukaci bawa yara maza da mata ilimi na bai daya mai inganci tun daga mataki na primary,kana a waje daya kuma da yaki da cutar kanjamau da Malaria bil hakki da gaskiya.
Ata bakin shugabar hukumar ta Unicef, wato Ann Venemann, daukar ire iren wadannan matakan itace hanya daya da za a inganta kasa da kuma ci gaban ta ta hanyoyi daban daban na rayuwarr dan Adam.