Rahoton Unicef a game da mutuwar ƙananan yara a dunia
September 13, 2007Hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia mai kulla da ƙananan yara, wato Unicef, ta bayyana rahoto a game da halin da yaran ke cikin dunia.
Wannan rahoto ya nunar da cewa, an samu ci gaba mai inganci, ta fannin rage yawan mace-macen ƙanana yara.
Yawan yaran da su ka mutu a sanadiyar cuwarawarta daban-daban a shekara da ta gabata, shine mafi ƙaranci tun shekarau 17 da su ka wuce.
Saidai wannan cigaba ya banbata, daga wannnan ƙasa zuwa wacen, sannan daga wannan nahia zuwa wacen.
A cewar hukumar Unicef, an cimma wannan kyaukyawan sakamako, a dalili da matakan da a ka ɗauka na waye kan jama´a, a game da mahimancin shayar da jarirai nono iyayen su, da kuma allurai riga kafi na cututukan gynda, da anfani ga gidajen sabro.
Rahoton ya yabawa wasu ƙasashen nahiyar Afrika, a game da nasara da su ka samu ta wannan fannin. Wannan ƙasashe sun haɗa da Malawi, Ethiopia, Jamhuriya Niger, Namibia da Tanzania.