1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Tanzaniya da muhallin yankin Ogoni a Najeriya

Umaru AliyuNovember 6, 2015

Siyasar kasar Tanzaniya da rahoton Amnesty kan yankin Niger Delta a Najeriya ke ciki na gurbatar muhalli sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1H1L5
Tansania Samia Suluhu und John Magufuli
Hoto: Getty Images/AFP/D. Hayduk

Ranar Alhamis ne aka yi bikin rantsar da sabon shugaban kasar Tanzaniya, John Magufuli, kan mukaminsa, bayan da ya lashe zaben kasar na karshen mako. Jaridar Neue Zürcher zeitung ta ce shi ne dan takarar da masu zabe a Tanzaniya suka fi son ya shugabancesu, saboda haka ne bayan kuri'un, hukumar zabe ta sanar da cewar shi ya sami nasara, duk kuwa da kararraki da tangarda da aka samu, abin da ya hada har da soke sakamakon zaben gaba daya a tsibirin Zanzibar. Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta tabo korafin da wadanda suka lura da zaben na Tanzaniya suka yi. Amirka misali, ta zargi hukumar zaben da laifin kin aiki da ka'idojin zabe, yayin da 'yan kallo na kungiyar hadin kan Turai suka ce ba su amince da tsarin da aka bi wajen kidaya kuri'un ba, inda sabon shugaba John Magulufi ya sami kashi 60 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Kungiyoyin kare hakkin 'yan Adam sun yi korafin cewar jami'an tsaro sun yi amfani da karfin da ya wuce kima domin tsoratar da 'yan adawa da 'yan kallo da suka tura wuraren kada kuri'u.

An zargi kamfanin Shell da karya kan yankin Ogoni

Ölquelle in Nigeria
Hoto: picture alliance/dpa

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland ta yi sharhinta ne kan sabon rahoton kungiyar kare hakkin 'yan Adam ta Amnesy International, a game da halin da yankin Niger Delta ke ciki. A rahoton nata, Amnesty ta zargi kamfanin Shell da laifin bada alkaluma da rahotanni na karya game da tsabtace yankin Nigr Delta da ya gurbace daga dattin man fetur a Najeriya. Amnesty ta ce hakan ya sanya kamfaninn na Shell ya keta sharuddan da Majalisar Dinkin Duniya ta shimfida shekara ta 2011, game da tsabtace wannany anki. Jaridar Neues Deutschland ta ce su kansu ma'aikatan kamfanin da Shell ya basu aikin tsabtace yankin na Niger Delta sun amince da cewar ba su yi wani aikin kirki ba, in banda kwashe dattin man fetur da ake iya gani a wuraren da abin ya shafa ba. Stevyn Obodoekwe, na cibiyar kiyaye muhalli da hakkin 'yan Adam da raya kasa, wanda yake daya daga cikin wadanda suka rubuta rahoton na Amnesty, ya yi suka a game da halin rayuwa a wuraren da dattin man fetur ya gurbata a yankin Niger Delta. Rahoton na Amnesty an fitar da shi ne yadda zai dace da cikar shekaru 20 da zartas da hukuncin kisa kan dan gwagwarmayar kare hakkin 'yan Adam Ken Saro Wiwa a yankin Ogoni, ranar 10 ga watan Nuwamba na shekara ta 1995.

Rigingimu sun ki ci sun ki cinyewa a Somaliya

Somalia Mogadischu Anschlag auf Hotel
Hoto: picture-alliance/AA/N. Gedi

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a sharhinta na wannan mako, ta tabo batun ayyukan tarzoma a Somaliya, inda wasu mahara suka tayar da bama-bamai a wani otel na birnin Mogadihu, tare da kashe mutane akalla 10, wasu kuma suka sami rauni. Kungiyar tarzoma ta Al-Shabaab da aka yi zaton ita ce take da alhakin kai wannan hari, ta amsa cewar a hakika mayakanta sun mamaye otel din bayan da suka tayar da bom a cikinsa, ko da shi ke shugaban 'yan sandan birnin Abdulrahid Dahir ya ce nan da nan aka ci karfin maharan bayan wani dauki ba dadi mai tsanani. Rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen AU a Somaliya, wato AMISOM, tana ci gaba da dauki ba dadi da mayakan Al-Shabaab da ke ci gaba da kai hare-hare a kasar ta Somaliya da kasashe makwabta.

Rashin majalisar ministoci a Najeriya

A karshe jaridar Berliner Zeitung ta yi sharhi kan rashin majalisar ministoci har yanzu a Najeriya. Jaridar ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari yanzu dai kusan watanni shida kenan yana mulki ba tare da majalisar ministoci ba, ko da shi ke bayan tankade da rairaya na lokaci mai tsawo da amincewar majalisar dokoki, akwai alamun a 'yan kwanakin nan shugaban zai bai wa wadanda ya zaba ma'aikatun da za su rike. Daga cikin zababbun kuwa, inji jaridar, akwai fuskokin da a zahiri ba sababbi ba ne, sai dai abin da ya zama mai ban mamaki shi ne daga cikin ministoci 36, shidda ne kawai mata.