1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: Majalisa ta yi kiran 'yancin gabashin Ukraine

Abdullahi Tanko Bala
February 15, 2022

Majalisar dokokin Rasha ta bukaci shugaba Putin ya amince da yankuna biyu da Rasha ke mara wa baya a gabashin Ukraine a matsayin kasashe masu cin gashin kansu.

https://p.dw.com/p/474cX
Russland Moskau | Sitzung der Duma
Hoto: Anton Novoderezhkin/Tass/imago images

Majalisar ta ce amincewa da yankin Donetsk da Luhansk zai kasance muhimmin mataki wanda zai kawo karshen shirin zaman lafiya na Minsk a gabashin Ukraine wanda Rasha ta amince da shi tun da farko.

Yunkurin Majalisar na hasashen bai wa yankunan biyu yancin cin gashin kai.

Kakakin majalisar dokokin na Rasha Vyacheslav Volodin ya ce 'yan majalisar za su yi kira ga kai tsaye ga Putin ya amince da yancin cin gashin kan na yankunan biyu a matsayin yantattun kasashe.