1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moscow ta yi fatali da zargin sa wa Navalny guba

Abdul-raheem Hassan
September 3, 2020

Dangantaka tsakanin Jamus da Rasha na tangal-tangal bayan da gwamnatin Berlin ta zargi Shugaba Putin da hannu a sa wa Alexy Navalny guba.

https://p.dw.com/p/3hx9c
Dmitry Peskov
Hoto: picture-alliance/Sputnik/S. Guneev

Jamus na shirin daukar matakai masu zafi idan fadar Kremlin ta yi martani mara dadi kan zarginta da hannu a rashin lafiyar madugun adawar kasar Navalny. Moscow ta yi watsi da duk zargin da ke alakanta Shugaba Vladimir Putin da yunkurin halaka jagoran adawar ta hanyar sa mishi guba, kamar yadda kakakin shugaban kasar Dmitry Peskov ke cewa:- 

"Zan yi magana ne kai tsaye kan zargin da ake wa Rasha. Babu wata hujjar yin haka, domin haka ba za mu amince da wannan zargi ba. Maganar gaskiya ma mun aike wa Jamus takardar neman taimaka wa Navalny, sun kuma karba amma ba su yi martani ba."

Alexy Navalny na kwance a wani asibitin sojoji da ke birnin Berlin a kasar Jamus tun bayan da ya kwanta rashin lafiyar mai cike da sarkakiya.