SiyasaTarayyar Rasha
Mutuwar Prigozhin ta sa ana zargin Rasha
August 25, 2023Talla
Yevgeny Prigozhin dai ya halaka ne a wani hadarin jirgin saman 'yan kasuwa, watanni kusan biyu bayan ya jagoranci wani yunkurin yin bore ga shugabannin rundunar sojojin Rasha. Yayin wani taron manema labarai da ya gudanar, mai magana da yawun Shugaba Vladmir Putin na Rashan Dmitry Peskov ya bayyana cewa ana yada jita-jita mai yawan gaske dangane da mutuwar fasinjojin da ke cikin jirgin da suka hadar da Prigozhin. Ya kara da cewa da ma tilas a yada wannan jita-jita da wata manufa a Kasashen Yamma, yana mai cewa duka karya ce zalla kawai.