Masu son haihuwa za su samu kudi mai tsoka
January 15, 2020Talla
A wani mataki na bunkasa yawan al'umma a kasar Rasha gwamnati ta sanar da karin kudin lada don karfafa gwiwar 'yan kasar kara hayayyafa. Da yake jawabin shekara ga majalisar dokokin kasar, Shugaba Vladimir Putin ya ce makomar kasar da tarihinta sun ta'allaka ne kan yawan al'ummarta da ke rayuwa a doron kasa.
Kasar Rasha na fuskantar raguwar karin hayayyafa tun bayan da fuskantar matsin tattalin arziki a shekarun baya. Shugaba Putin wanda ke da 'ya'ya biyu mata, ya danganta talauci a matsayin abin da ke hana mutane zuba yara.