1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kame masu zanga-zanga a Mosko

July 29, 2019

Mutane da dama suka sami raunika sannan har yanzu wasu daruruwa na tsare bayan artabu tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga a birnin Mosko.

https://p.dw.com/p/3MuHb
Russland Moskau Protest Opposition Polizei
Hoto: Reuters/M. Shemetov

Dubban masu zanga-zanga ne suka mamaye babban dandalin da ke birnin na Mosko fadar gwamnatin kasar ta Rasha, suna nuna rashin jin dadi da matakin gwamnati na cire sunayen 'yan takara masu zaman kansu a zaben majalisar karamar hukumar birnin na Mosko da aka tsara gudanarwa a ranar 8 ga watan Satumba da ke tafe. Tun a ranar Lahadi an saki mafi yawan mutane daga cikin kimanin mutane 1,400 da hukumomi suka kama.

Tun farko hukumomi sun yi gargadin yin zanga-zanga da ta saba doka. Sannan suka ce za su dauki mataki kan duk wanda ya saba doka. Duk da haka an samu dubban mutane da suka fito kamar wannan matashin da ke ciki:

"Ina jin tsoro. Na gaji da zama cikin tsoro. Wadanda ke kan madafun iko suna wasa da hankalin mutane. Suna cin zarafin mutane."

Ita hukumar zaben ta kuma ki yin rajista ga 'yan takara 58 na bangaren adawa domin shiga zaben da ke tafe. Akwai tsaffi gami da iyalai da kuma 'yan makaranta da suka shiga zanga-zangar ta birnin Mosko. Sun hada kai waje daya. Suna son hukumomi su san da gaske suke yi. Suna neman samun tacewa kan zabin wanda zai lashe zaben, kuma wannan matar tana ciki:

"Ina fada kan kare hakkina ne, saboda babu 'yancin kada kuri'a a wannan kasa wanda muke bukata, domin yin zabi kan abin da muke muradi."

Jagoran 'yan adawa Alexei Navalny lokacin wani gangami a birnin Mosko
Jagoran 'yan adawa Alexei Navalny lokacin wani gangami a birnin MoskoHoto: DW/S. Dick

Shi kansa jagoran 'yan adawa Alexei Navalny an sallame shi daga abisiti, kuma 'yan adawa suna zargi guba aka saka masa. Tun a makon da ya gabata wata kotu ta daure jagoran 'yan adawar na Rasha kwanaki 30 a gidan fursuna saboda ya kira zanga-zangar da ta saba ka'ida. Daya daga cikin masu zanga-zangar ta nuna takaicin yadda aka cire sunanta daga cikin 'yan takara na majalisar karamar hukumar birnin Moko, duk da cika sharudda da ta yi.

"A gundumarmu ta Gudlov, zan tabbatar kashi 100 cikin 100 aka samu tabbatar da saka hannunsu daga makwabta da suka tattaru a gabanmu a kan idona."

'Yan sanda sun ce kimanin mutane 3,500 suka shiga zanga-zangar, amma hotunan masu zanga-zangar da aka dauka daga sama sun tabbatar da cewa masu zanga-zangar sun kai 8,000. Shi dai Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya fice daga birnin na Mosko gabanin zanga-zangar, inda ya kai ziyara wajen babban faretin sojojin ruwa a birnin St Petersburg. Faretin da ya hada da jiragen ruwan yaki 43 gami da sojojin kundunbala na ruwa 4,000.