SiyasaJamus
Rasha: Amirka ba ta da muradin inganta hulda
March 18, 2021Talla
Wannan batun dai ya haifar da rikici mafi girma a 'yan shekaru tsakanin kasashen Amirka da Rasha da har yanzu suke yakin cacar baki. A zantawarsa da manema labarai, shugaba Joe Biden na Amirka ya ce za su dau mataki kan kokarin yin katsalandar da Rasha ta yi ga zaben da ya gudana a shekarar 2020 da ya bai wa Biden din nasara.
A nata martanin, Rasha ta ce za ta janye jakadanta da ke Amirka don tattaunawar gaggawa, matakin da ba a taba ganin irinsa ba a diflomasiyyar Rasha ta baya-bayan nan.
Alakar Rasha da kasashen Yamma ta tabarbare sakamakon yawan rashin jituwa, amma dangantakar ta dauki wani sabon babi biyo bayan kalaman shugaba Biden a ranar Laraba.