Rasha ta dakatar da cinikin Dala da kuma Yuro
June 13, 2024Talla
Gwamnatin Washington ta sanar da cewa ta sanya takunkumi kan kasuwar hada-hadar kudaden kasashen waje na Rasha a matsayin sabuwar hanyar ladabtar da ita, sakamakon sabbin hare-hare da ta kai Ukraine.
Ana dai ganin cinikin kudaden kasashen waje shi ne babban madogar tattalin arzikin Rasha. Sakamakon faduwar darajar kudin kasar na rubles cikin shekaru 30 da suka gabata, tun bayan rushewar tsohuwar tarayyar Soviet, 'yan Rasha ke yin ajiyarsu da kudaden kasashen waje a lokacin matsin tattalin arziki.