1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta kai harin Zaporizhzhia

October 6, 2022

Rahotannin daga yankin Zaporizhzhia da ke gabashin Ukraine, na nuni da cewa Rasha ta kaddamar da harin roka kan wasu gine-gine.

https://p.dw.com/p/4HqbQ
Ukraine | Ma'aikata na aikin ceto a Zaporizhzhia
Hoto: Ukrainian Emergency Service/AP/picture alliance

Gwamnan yankin Oleksandr Starukh ya ce wasu mutane biyar sun makale cikin barakuzan gine-ginen. Harin na zuwa ne sa'o'i kalilan bayan da shugaban Ukraine Volodmyr Zelensky ya sanar da sake kwace iko da wasu kauyuka uku a yankin. Yankin na Zaporizhzhia da ke karkashin ikon Ukraine, na daga cikin yankuna hudu da Rasha ta shigar kasarta. A ranar Larabar da ta gabata dai, Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya rattaba hannu kan dokar da ke nuna cewa Moscow za ta karbe ikon tashar nukiliyar yankin.