Rasha ta karfafa tsaro a Baltik
July 2, 2016Talla
Ministan tsaron na Rasha ya sanar da daukar wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Asabar din. Kasashen yankin Baltic da ke makotaka da kasar ta Rasha da kuma ke kasancewa mambobin kungiyar NATO da kuma ma'aikatan tsaron Amirka ta Pentagon na yawan zargin Rasha da keta haddin sararin samaniyar kasashen yankin na Baltic da yin shawagi a saman tekun Baltic ta hanyar kashe na'urar da ke bai wa na'urar da ke sa ido ga zirga-zirgar jirage a sama bin tafiyar jiragen sama don hana musu yin karo da juna, a yayin da daga nata bangare Rashar ke zargin Amirka da yin amfani ita kanta da jiragen masu layar zana a yankin.