1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Al'amura na kara rincabewa

Lateefa Mustapha Ja'afar
April 28, 2023

Bangarorin da ke yakar juna a Sudan na kokarin tsawaita wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta, domin kawo karshen rikicin kusan makonni biyu da ya lakume rayuka da dama tare da barnata dukiya.

https://p.dw.com/p/4QgVy
Sudan | Khartum | Yaki
Birnin Khartoum ya zamo tamkar kufai, sakamakon yakiHoto: AFP/Getty Images

Rahotanni sun nunar da cewa a yankin Darfur wanda da ma ya yi kaurin suna a rikici, likitoci sun bayyana mutuwar kimanin mutane 74 cikin kwanaki biyu da aka kwashe ana gwbza fada a birnin El Geneina. Ana dai hango yadda bakin hayaki ke tashi a babban birnin kasar Khartoum, a daidai lokacin da kasashen ketare ke kokarin kwashe al'ummominsu daga kasar da yaki ke ci gaba da daidaitawa. Tun bayan da yaki ya barke a tsakanin sojojin gwamnati karkashin jagorancin Janaral Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun RSF karkashin jagorancin tsohon mataimakinsa kana abokin burminsa a yayin juyin muilkin da sojojin suka yi a kasar Mohamed Hamdan Daglo a ranar 15 ga wannan wata na Afrilu da muke ciki, ake ta kai kawon ganin an sasanta su amma abin ya ci tura.