1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas game da siyasar Sudan

Mohammad Nasiru Awal ZU
March 13, 2020

Jaridun Jamus sun dubi rikicin siyasar Sudan da batun kawo karshen cutar Ebola a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

https://p.dw.com/p/3ZMD1
Abdalla Hamdok
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Jaridar Die Tageszeitung ta yi tsokaci kan harin da aka kai kan Firaministan Sudan Abdallah Hamdok tana mai cewa harin da bai yi nasara ba da aka kai wa Firaministan na Sudan na nunawa karara cewa akwai rashin tabbas a wannan lokaci da ake kokarin kai kasar ga tsarin mulkin dimukuradiyya. Shaidun gani ido sun ce wani bam ya fashe a kan wata gada daidai lokacin da ayarin motocin Firaministan suka tinkari wajen. Bam din ya lalata motoci da dama an kuma yi harbe-harbe amma babu abin da ya taba lafiyar Firaminista Abdalla Hamdok, wanda ma ya tabbatar da cewa yunkurin kisan nasa ba zai sa ya yi kasa a gwiwa ba a matakan da ake dauka don kawo sauyi a kasar ta Sudan. Ko da yake ba a san masu hannu a harin ba amma kungiyar kwararrun ma'aikata da ta taka rawa a zanga-zangar da ta yi sanadin kawo karshen mulkin Omar al-Bashir ta ce a fili yake yunkurin wani kokari ne na dakatar da juyin juya halin da kasar ke ciki.

Sudan Anschlag auf den Premierminister in Khartoum
Wajen da aka kai wa Firaministan Sudan hariHoto: Reuters/M.N. Abdallah

Ita ma jaridar Neues Deutschland ta yi sharhi kan batun na Sudan tana mai cewa Sudan na cikin wani wadi na tsaka mai wuya inda a karshen shekara rundunar sojin kasar za ta mika ragamar mulki gaba daya ga farar hula. Saboda haka abin da ya faru a ranar Talata ka iya zama wata makarkashiya da makiyyan Hamdok suka kulla don jefa kasar cikin rudani ta yadda watakila sojoji za su iya amfani da wannan dama don ayyana dokar ta-baci. Jaridar ta ce da wuya a iya yin hasashe ko gwamnatin wucin gadin za ta wanye lafiya har a kai ga kafa sahihin tsari na dimukuradiyya. Ta ce dole sai an magance wasu kalubale a cikin watanni masu zuwa kafin mulki ya fita hannun sojin kasar.

Symbolbild Masernkrise
An sallami majiyancin Ebola na karshe a kasar KwangoHoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Daga batun siyasa sai na kiwon lafiya, inda jaridar Frankfuter Allgemeine Zeitung ta ce a birnin Beni na kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango an sallami mai jinya na karshe daga cibiyar kula da masu cutar Ebola. Jaridar ta ce wannan labari ne mai dadin ji kasancewa an kai mataki nakarshe a kan cutar wace ta addabi kasar a shekarun baya-bayan nan. Sai dai hakan na zuwa ne daidai lokacin da duniya ke fama da annobar cutar Coronavirus. Jarida ta kara da cewa za a ci gaba da tsare mutane 46 da suka yi hulda da majinyacin da aka sallama, domin sa ido a kansu. Za a iya ayyana kawo karshen cutar ta Ebola a hukumance idan aka kwashe kwanaki 42 ba tare da an samu wani da ya harbu da ita ba.