Ghana: Rawar matasa a babban zabe
December 5, 2024Sama da matasa dubu 480 ne ake sa ran zasu kada kuri'a a karon farko, a babban zaben da za a gudanar a karshen mako a kasar Ghana. Alkaluman Hukumar Zaben kasar ne suka tabbatar da adadin matasan, wadanda ake ganin za su iya taka rawar gani wajen fitar da wanda zai yi nasara a zaben shugaban kasa. A shekarun baya galibi matasan da ke kada kuri'unsu a karon farko kan bi ra'ayin iyayensu ne, ko kuma wata nasaba da suek da ita da wata jam'iyya ko dan takara. Sai dai a wannan karon ma kamar kowanne lokaci, akwai takaddama tsakanin mayan 'yan takarar shugabancin kasar biyu da suka kasance Musulmi da Kirista. Sai dai kuma duk da yadda ake ganin siyasar Ghana na neman karkata zuwa ta addini, manyan 'yan takarar biyu dai sun mayar da hankali a gangamin yakin neman zabensu kan bunkasa harkokin ilimi da ma batun bayar da shi kyauta musamman ga matasa.