Rayuwar 'yan gudun hijirar Najeriya a Nijar
March 19, 2014'Yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya koro daga Jihohin Arewa masa gabashin Tarayyar Najeriya da yawan su ya haura 40 000 suna jibge ne a garuruwan da dama na jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar. A yayin da DW ta zanta da wasu daga cikinsu dake garin Diffa, halin da suke ciki suka bayyana. A yayin da daddadu ke hamdalla biyo bayan cin moriyar tallafin kungiyoyin agaji da suka yi, su kuwa sabbin zuwa halin kuncin da suke ciki suka bayyana.
Amsatu Musa wata magidanciya da ke rike da kananan yara marayu 'yan shekaru daga biyar zuwa bakwai, wadanda rikicin ya hallaka mahaifansu, korafi tayi game da jinkirin zuwan tallafin.
A daidai lokacin da 'yan gudun hijira ke cikin garari, shugaban kungiyar agaji ta Croix Rouge ko Red Cross kira ya yi don neman daukin kasa da kasa. A yanzu haka dai kungiyar na hankoron ganin 'yan gudun hijirar Najeriya a Nijar sun samu taimakon da ya dace daga abinci har i zuwa kudaden gudanar da kasuwanci da kuma na sana'o'in hannu don samun na sakawa a bakin salati.
Gwamnatin Nijar ta taimaka wajen karbar 'yan gudun hijirar Tarayyar Najeriya wanda rikicin Boko Haram ya ritsa da su. Sai dai kuma duk da ikirarin da kungiyoyin agaji ke yi ta hanyar mika tallafi, da dama daga cikinsu na ikirarin cewa tallafin bai kaiwa garesu. Tuni dai Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta HCR tare da kungiyar agaji ta Croix Rouge ta kasar Nijar suka kudiri aniyar girka gidauniyar neman dauki a matakin farko na kula da lafiyar 'yan gudun hijirar.
Mawallafi Larwana Malam Hami daga Diffa
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe