Red Cross ta tsaida aiki a Afganistan
April 11, 2019Talla
Matakin kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross na zuwa ne bayan barazanar da kungiyar Taliban ta sanar na haramta ayyukan kungiyoyin agaji na Red Cross da hukumar lafiya ta duniya a Afganistan.
Taliban ta zargi kungiyoyin da saba yarjejeniyar aiki a yankunansu tare da tuhumar hukumar lafiya ta duniya da leken asiri yayin gudanar da gangamin rigakafi.
Kawo yanzu babu martani daga bangaren WHO kan wannan mataki da Taliban ta dauka, sai dai akwai fargaba matakin zai shafi dubban mutanen karkara da ke fama da cutar shan inna.
Kasashen Afganistan da Pakistan da Najeriya na cikin kasashen da ake yawan samun bullar cutar polio akai akai duk da cewa alkaluma na nuna raguwar cutar da kashi 99 tun shekarar 1988.