Riek Machar ya fice daga Juba
August 18, 2016Talla
Riek Machar ya fice ne sakamakon yadda aka dakatar da shirin sulhu na tattaunawa tsakanin gwamnatin da 'yan tawaye.Wasu na kusa da shugaban sun ce ya yi hijira a cikin wata kasa da ke a yankin gabashin Afirka inda ake da tabbacin tsaro lafiyarsa.
Tun farko jagoran 'yan adawar ya bukaci kwamitin sulhu na MDD ya tura wata runduna sojoji ta shiga tsakanin to sai dai shugaban Salva Kiir bai amince da haka ba.