Riek Machar ya zama sabon mataimakin shugaban Sudan ta Kudu
April 27, 2016Hakan dai na zuwa ne bayan da dukkanin bangarorin biyu wato tsakanin tsohon dan tawayen da kuma shugaban kasar Salva Kirr suka kai ga cimma daidaito domin samun dorewar zaman lafiya a kasar.
Kazalika Sabon mataimakin shugaban kasar ya kuma godewa Shugaba Salva Kirr a bisa na dashi mukamin na biyu a kasar data dauki tsawon lokaci tana fama da rikice rikece tsakanin bangarorin biyu.
Shirin yarjejeniyar tsagaita wutar da Majalisar Dinkin Duniya take shiga tsakani shine ya bayar da damar rantsar da Riek Machar a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa gami da girka sabuwar gwamnatin hadin gambiza.
Tun dai a shekara ta 2013 sai da Riek Machar ya taba zama matimakin shugaban kasa kafin kasar ta Sudan ta Kudun ta fantsama cikin yakin basasar daya tilastawa daruruwan 'yan kasar neman mafaka a makwafciyar kasar ta Sudan .