Takaddama tsakanin Falasdinu da Isra'ila
January 3, 2023Talla
Ministan ya kai ziyarar ne duk da barazanar da Hamas da Falasdinu suka yi tun can da farko kafin ziyarar, Ziyarar ministan mai tsatsaurar ra'ayi ta janyo martanin mai zafi na bangarorin gwamnatin Falasdinu da Hamas. Ma'aikatar harkokin wajen Falasdinu ta fitar da wata sanarwa yin Allah wadai da ziyarar a masallacin na Al-Aqsa. Abin da ta kira da cewar tsokana ce. Masallacin da ke a birnin Kudus na cikin yankin Falasdinu wanda Isra'ila ta mamaye tun a shekarar ta 1967.