1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rigimar Sudan ta dauki hankalin jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal MA
February 1, 2019

A kasar Sudan, ana ci gaba da zanga-zangar adawa da Shugaba Omar al-Bashir amma har yanzu shugaban ya ki sauka. 'Yan kasar dai sun ce sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.

https://p.dw.com/p/3CZKx
Sudan Khartum Kundgebung Anhänger von Präsident Al-Baschir
Hoto: picture-alliance/AP Photo/M. Hjaj

A wannan makon za mu fara sharhi da labarun jaridun Jamus kan nahiyar Afirka da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta ce zanga-zangar da ta samo asali bayan da gwamnati ta kara farashin burodi amma ta rikide ta zama na neman Shugaba al-Bashir da tun a 1989 yake kan mulki, ya yi murabus an shafe sama da makonni biyar ana yi. Jaridar ta ce wannan ba shi ne karon farko a tarihin kasar wani boren al’umma ya yi sanadin sauyin gwamnati ba. A 1964 wani boren al’umma ya yi awon gaba da Shugaba Ibrahim Abbud sannan a1985 irin wannan ta faru ga Shugaba Jafar an-Numeiri. A kwanakin da suka wuce an jiyo al-Bashir na fada wa sojojin kasar cewa zai sauka daga karagar mulki ne idan aka ya fadi a zabe ko kuma idan sojoji ne suka yi kifar da gwamnatinsa. Wato ke nan ba shi da niyar mika wuya ga masu zanga-zangar adawa da mulkinsa duk da matsin lambar da yake fuskanta daga dukkan bangarorin kasar.

 

Ghana Anas Aremeyaw Anas Undercover-Journalist
Anas Aremeyaw Anas, dan jarida mai binciken kwa-kwaf a GhanaHoto: DW/H. Fischer

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel a wannan makon labari ta buga game da dan jaridar nan na kasar Ghana wato Anas Aremeyaw Anas wanda ya shahara wajen bankado labarai na take hakkin dan Adam da cin hanci da rashawa a Afirka. Jaridar ta ce Anas ya lashi takobin ci gaba da wannan aiki duk da barazanar da yake fuskanta shi kanshi.

 

A baya bayan nan an yi wa abokin aikinshi kisan gilla a birnin Accra dangane da badakalar da suka gano a fannin kwallon kafa a nahiyar Afirka. Sama da shekaru 10 ke nan dan jaridar ke wannan aiki yana da kuma farin jini a wajen talakawa da sauran manyan shugabannin duniya, sai dai masu iko da fada a ji a Afirka sun tsane shi. A gare shi aikin jaridar shi ne fadin gaskiya komai dacinta zai kuma ci gaba da yin haka har sai ya ga abin da ya ture wa Buzu nadi.

 

Yanzu kuma sai jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta leka kasar Senegal inda aka bude wani katafaren gidan adana kayakin tarihi mai suna wayewar kan bakar fata da ke nuna ainihin yadda nahiyar Afirka take ba da wani nakasu na mulkin mallaka ba. Jaridar ta ce gidan kayan tarihi na birnin Dakar da aka bude a farkon watan Disamban 2018, na zama irinsa na farko kuma mafi girma da aka yi masa salon gini iri na bukkoki don fito gargajiyar Afirka tun gabanin zuwan Turawan mulkin mallaka a nahiyar. Jaridar ta ce yanzu hujjojin da ake da’awar cewa ba za a iya mayar wa Afirka kayakin tarihinta da aka sace zuwa kasashen Turai ba saboda rashin gidajen tarihi da suka dace, yanzu sun kau musamma ga kasar Senegal saboda sabon gidan tarihin nata mai isasshen fili da ke bukatar a cike su da kayan tarihi.