1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici Isra'ila da Hamas na rintsabewa

Mouhamadou Awal Balarabe
May 16, 2021

Kungiyar Hamas da sojojin Isra’ila na ci gaba da kai wa juna hare-haren da ke salwantar da rayuka. Hamas ta sake harba rokoki kan Isra'ila, yayin da Isra’ila ta yi ruwan bama-bamai a gidan shugaban Hamas da ke Gaza.

https://p.dw.com/p/3tS7b
Palästina Gazastreifen | Beit Lahia | Israelische Luftschläge in der Nacht
Hoto: Mohammed Abed/AFP/Getty Images

Kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta Falasdinawa wato Hamas ta sake harba rokoki kan Isra'ila a daren Asabar zuwa Lahadi, a cewar rundunar sojojin kasar Isra'ila. Ba a dai ba da rahoton ko harin ya salwantar da rayuka ko jikkata mutane ba ya zuwa yanzu. Amma a nasu bangaren, wasu majiyoyin Falasdinawa sun bayyana cewa sojojin saman Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a gidan shugaban Hamas da ke Gaza, inda akalla mutane uku suka mutu yayin da wasu da dama kuma suka jikkata. 


Duk yunkuri da kasashen duniya ke yi don  ganin an shawo kan wannan rikici da ke haddasa zubar da jini bai cimma nasara ba ya zuwa yanzu. Shugaban Amirka Joe Biden ya tattauna da Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a karon farko, inda ya nuna “damuwarsa” kan karuwar tashe-tashen hankula a Isra’ila da Gaza. Yayin da a daya hannun kuma ya nema daga Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas cewa kungiyar Hamas ta “daina harba rokoki a kan Isra'ila”.