1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Rikici ya kazanta a Khartum da Darfur

April 29, 2023

Yayin da a wannan Asabar aka cika mako na biyu da barkewar rikicin Sudan, sojojin da ke biyayya ga manyan habsan sojan biyu masu kokowar iko sun ci gaba da lugudan wuta a tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/4Qhma
Hoto: Mahmoud Hjaj/AA/picture alliance

Duk da sabunta kwarya-kwaryar yerjeniyar tsagaita buda wuta da ake rattaba bisa jagorancin Amurka, bangarorin manya habsan sojan biyu sun kwan daren Jumma'a wayewar Asabar suna barin wuta a Khartun da kuma Darfur.

Rikicin da ya fara daga Khartun babban birnin kasar Sudan ya bazu a ranar Litinin din da ta wuce izuwa Darfur inda a cikin kwana biyu kadai a ka samu mutuwar mutane 74 a kididdigar wucin gadi da kungiyar likitocin kasar ta fitar.

Msu aiko da rahotanni daga sassa daban-daban na Sudan din sun ce wannan rikici da kawo yanzu ya yi ajalin mutane 500 tare da raba dubbai da matsugunensu ya jefa miliyoyin al'umma cikin halin kunci rayuwa na rashin wutar lantarki da ruwan sha, baya ga tsayawar harkokin jinya a gidajen asibitoci.

A jiya Juma'a mayan habsan sojan masu sun yi bayanai a kafafen sadarwa inda suka zargi junansu da kin mutumta yerjejiyonin tsagaitai wuta. Hasali ma sojoji masu biyayya ga janar Burhane sun zargin sojojin Tchadi da na jamhuriyar Afrika ta Tsakkiya da kuma Nijar da shiga bayan abokan fadansu na RSF dake karkashin janar Daglo.