1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na kara kamari a Gaza

Gazali Abdou Tasawa
November 13, 2019

Mutane akalla takwas ne suka halaka a cikin wasu sabbin hare-hare da jiragen yakin Isra'ila suka kaddamar a wannan Laraba a sansanin kungiyar masu da'awar Jihadi ta Jihad Islamique da ke Gaza.

https://p.dw.com/p/3Sw81
Israel - Palästina - Konflikt l Raketenangriffe auf Israel
Hoto: picture alliance/AA/A. Amra

Mutane akalla takwas ne suka halaka a cikin wasu sabbin hare-hare da jiragen yakin sojojin Isra'ila suka kaddamar a wannan Laraba a sansanin kungiyar masu da'awar Jihadi ta Jihad al Islami da ke a Zirin Gaza wacce daga nata bangare ke ci gaba da ruwan rokoki zuwa biranen Isra'ila masu makobtaka da yankin na Gaza inda ya zuwa yanzu ta harba rokoki kimanin 250.

Wannan dai ya biyo bayan wani farmaki ne da sojoji da kuma jami'an leken asirin cikin gida na kasar ta isra'ila suka kai a jiya Talata a yankin na Gaza inda suka halaka Baha Abou al-Ata wani babban kwamandan kungiyar ta Jihad al Islami da matarsa Asma.

Ya zuwa yanzu dai Falasdinawa 18 ne da suka hada da mayakan al-Qods na kungiyar ta Jihadi al Islami suka halaka tun bayan sake barkewar rikicin wanda ke kara ta'azzara a wannan Laraba.

 Yanzu haka dai illahirin makarantu tun daga na reno har ya zuwa jami'o'i sun kasance a rufe a biranen Isra'ilar da dama da suka hada da birnin Tel-Aviv a sakamakon hare-haren rokokin.