Rikici tsakanin sojojin Angola da Kwango
October 19, 2013Talla
Jami'an tsaron Angola sun saki sojojin Jamhuriyar Demokaradiyar Kwango 55 da suka kame a ranar Litinin din da ta gabata a yankin Kimongo dake kan iyakar kasashen biyu, inda suka tsaresu a kasar ta Angola.
Wani babban jami'in gwamnati daga gundumar Niari a Jamhuriyar Demokaradiyar Kwangon Jacques Mouanda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sun yi amfani ne da hanyar diplomasiya, kafin suka samu aka sako sojojin.
'Yan tawayen kasar Angola dake makwabtaka da Kwangon na da'awar cewa shi yankin na Kimongo mallakinsu ne.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe