Fiye da mutane 180 sun mutu a rikici
April 18, 2023Rahotanni daga kasar Sudan na nuni da cewa fiye da mutane 180 suka halaka yayin da wasu kusan 2000 suka jikata sakamakon artabu da ake ci gaba da fafatawa tun karshen mako tsakanin sojojin kasar da dakarun hukumar tsaro mai karfi.
Shugaban mayakan kungiyar tsaro ta ko ta-kwana RSF, mai karfi, Janar Mohamed Hamdan Dagalo wanda aka saninsa da Hemedti ya tabbatar da shirin dakarun na mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwana daya domin fararen hula da rikicin ya ritsa da su samu hanyar ficewa. Wasu rahotannin kafafen yada labarai na kasashen Larabawa sun nuna cewa yarjejeniyar ta fara aiki, inda lamura suka lafa bayan fafatawa tun ranar Asabar da ta gabata.
Sai dai Janar Hemedti ya zargi sojoji da rashin mutunta yarjejeniyar wajen kai hare-hare yankunan da ke shake da fararen hula.
Wannan rikici na Sudan ya samu asali sakamakon sabani tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan shugaban hafsoshin soja kuma shugaban gwamnatin rikon kwarya da shugaban mayakan kungiyar tsaro ta ko ta-kwana RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo kana mataimakin shugaban gwamnatin.