Mutum 24 sun mutu a Darfur na Sudan
April 13, 2023Talla
Kimanin mutane 24 ne aka halaka a wani rikicin kabilanci a yankin Darfur na Sudan. Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce rikicin ya kaure tun a ranar Asabar din da ta gabata a tsakanin Larabawa da wasu kabilu.
Kawo yanzu hukumomin kasar sun ayyana dokar hana fita da daddare domin shawo kan rikicin da ya yi sanadiyyar kona gidaje 50 a yankin.