1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Darfur

Zainab A MohammadApril 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bu0S
Sansanin yan gudun hijira na Darfur
Sansanin yan gudun hijira na DarfurHoto: AP

Wakilan gwamnatin sudan na bukatar tattaunawar ido na ganin ido da shugabannin yan tawaye daga lardin Darfur,adangane da kwarya kwaryar yarjejeniyar sulhu da kungiyyar gamayyar Afrika ta gabatar musu,adai lokacin da waadin ranar lahadi ke gabatowa.

Tattaunawar warware rikicin darfur domin cimma yarjejeniya,tsakanin gwamnatin Sudan da yan tawayen lardin darfur ya dauki kusan shekaru biyu kenan yana tafiyar hawainiya ,a fadar gwamnatin Nigeria dake Abuja.A yanzu haka dai bangarorin biyu na fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya a dangane da kawo karshen rikin daya dauki shekaru 3 yana gudana a yammacin Sudan.

A ranar talata da dare nedai kungiyar Au mai shiga tsakani,ta gabatar musu da kwarkwaryar yarjejeniyar sulhu,domin gaggauta cimma wata madafa kafin waadin 30 ga wannan wata da aka tsayar musu.

Yarjejeniyar mai shafuna 85 dai,ya kunshi bastutuwa na tsaro da raba mukaman gwamnati dakuma dukiyar kasa,wadanda ke kasancewa jagorai wajen gano bakin zaren warware rikicin lardin na darfur.

Kakakin gwamnatin Sudan ,kuma wakili a zaman suhun Amin Hassan Omar,ya bayyana takardar yarjejeniyar da kasancewa tubali mai nagarta,dazai samarda da matashiyar tattaunawa da yan tawayen.

Ya kara dacewa suna cigaba da tattaunawa da kungiyoyin yan tawayen biyu,domin samar da hanya mafi sauki na shawo kann matsalolin da suka hana ruwa gudu wajen warware wannan rikici.

A yan makonni da suka gabnata dai,rahotannin sun tabbatar dacewa shugabannin bangarin adawan sun fara tuntubar juna ido da ido,domin a mafi yawan lokuta cikin shekaru biyu da suka gabata,suna tattaunawa ne ta hanyar masu shiga tsakani na kungiyar AU,amma ba kai tsaye da junansu.

Majiyar gwamnatin Sudan din dai na nuni dacewa mataimakin shugaban kasa Ali Osman Mohammed Taha na shirin ganawa ido da ido da Minni Minnawi,shugaban kungiyar yan tawaye mafi karfi ta SLA.

Komowar Minnawi zuwa Abuja a yan makonnin na ,bayan kin bayyana na watanni da dama,na nuni da alamun cigaba da aka samu a dangane da wannan rikici.

Matsalar dai a halin yanzu itace,cigaban fada tsakanin bangarorin adawa da juna na kungiyoyin yan tawayen.

A shekara ta 2003 nedai kungiyar SLA da JEM mafi kankanta,suka dauki makamai a wani rikici dake zama na kabilanci a Darfur,lardin da girmansa yakai kasar faransa baki daya,adfan gane da abunda suka kira wariyar da banbancin launin fata daga bangaren gwamnatin sudan ,dake da rinjayen larabawa farare.Wannan rikici dai ya haddasa asaran dubban rayuka,baya ga fyade da dibar ganima lokacin yaki,ayayinda aka kiyasta cewa mutane million 2 ne suka yi gudun hijira daga matsugunnensu.