Tsamin dagantaka tsakanin Najeriya da Nijar
December 20, 2024Rikicin diplomasiyyar da ya hada kasashen Nijar da Najeriya tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar a watan Yulin 2023 ya soma daukar wani sabon salo, bayan da hukumomin kasar ta Nijar suka gayyato jakadan Najeriya a birnin Yamai, inda suka nuna masa bacin ransu ga kasar ta Najeriya wacce suke zargi da ci gaba da hada kai da wasu kasashen duniya makiyan Nijar da kuma jami'an hambararriyar gwamnatin Bazoum wajen tayar da zaune-tsaye a kasar ta Nijar.
Sai dai tuni wasu ‚yan Nijar suka fara kiraye-kiraye kan a kai zuciya nesa da bin hanyar sulhu wajen shawo kan wannan rikici diplomasiyya da wasu ke ganin shi ne mafi girma a tarihin kasashen biyu 'yan uwan juna tun bayan samun 'yancin kansu. A halin da ake ciki dai hukumomin Najeriya ba su ce ufan ba har yanzu bayan gayyatar jakadinsu a Nijar.