Rikicin garin Kubane na kasar Siriya
January 14, 2015Garin Kubane na kasar Siriya ya fuskanchi barazanar yan tada kayar baya na kusan watanni hudu tun bayan da mahara suka addabi garin ta hanyar kai hare-hare masu tada hankali, duk da cewa dakarun Kurdawa wadanda ke da goyon bayan hadakar jiragen yaki da kuma rundunar tsaro ta kasar Iraki sun dauki matakin kare garinsu, amma hakan bai hana an daina samun fadace-fadace ba.
Yin jana'izar gawawwaki ya zama ba sabon abu ba a wannan gari cikin wadannan kwanaki, sakamakon tashe-tashen hankula na yau daban, na gobe daban, wanda hakan ya haifar da zullumi da tsoro a zukatan mazauna garin. Jana'izar Ahmed Abut da dansa Mustafa mai shekaru goma sha hudu ta gudana, bayan duk an kashe su a lokaci da ISIS suka kawo hari tare da tarwatsa gidan su da ke kudancin Kubane.
Da yake a yanzu duk shagunan da ake sayar da kayan masarufi babu su a Kubane, mahukunta a matakin karamar hukuma su ne suka dauki gabaren tallafawa mazauna garin da Abinci, da kayan sawa kai har da magunguna.
Pewer Mohammed Ali dan jarida ne mai kimanin shekaru 27 da ke garin na Kubane, ya ce barnar da aka yi a wannan gari ba za ta musaltu ba, kuma duk da cewa Ali ya san zaman sa a wannan alkarya yana da matukar hadari, amma ya ce akwai nauyi a kansa na ya tsaya.
Minstan tsaro na yankin Kubane Ismat Sheikh Hasan, ya ce fadan da ake gwabzawa, yafi karfin jurewar yawan jama'ar da ke garin.